13 Maris 2021 - 13:54
Iran:Majalisar Dokokin Kasar Ta Yi Wastsi Da Shawarar Komawa Kan Yarjejeniyar JCPOA Mataki-Mataki

Shugaban kwamitin tsaron kasa da kuma al-amuran harkokin waje na majalisar dokokin kasar Iran Mujtaba Zunnur ya bayyana cewa batun komawar Iran kan yarjejeniyar JCPOA mataki-mataki kamar yadda wasu suka bada shawarar a yi, bai sami amincewar kwamitansa ba.

ABNA24 : Tashar talabijin ta Al-Alam a nan Tehran ta nakalto Zunnur ya na fadar haka a wata hira ta musamman wacce ta hada shi da tashar.

Zunnur ya ce dole ne gwamnatin kasar Amurka ta dauke dukkan takunkuman tattalin arzikin da ta dorawa kasar Iran, kafin Iran ta fara komawa kan yarjejeniyar ta JCPOA.

Har’ila yau AmirAbadi Farohani mamba a kwamitin ya bayyanawa Al-Alam kan cewa shawarar komawa kan yarjejeniyar JCPOA mataki-mataki ba karbabbiya bace a wajen majalisar, sannan gwamnatin kasar Iran ba zata sabawa umurnin majalisar ba.

Iran za ta ci gaba da nisantar yarjejeniyar ta JCPOA matukar mutanen kasar ba za su amfana da ita ba, inji shi.

342/